Zan yi iya yina kan zawarcin Bale - Mourinho

Gareth Bale da Zinedine Zidane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bale ya taimaka wa Madrid ta dauki kofin Zakarun Turai da La Liga a karkashin Zinedine Zidane

Kociyan Manchester United Jose Mourinho ya ce zai fafata da sauran koci-koci domin sayen Gareth Bale idan har Real Madrid za ta sayar da dan wasan gaban na Wales.

A 2013 Bale, mai shekara 28, ya koma Real Madrid a kan kudin da ya fi wanda aka taba sayen duk wani dan wasa a duniya a lokacin fam miliyan 85 daga kungiyar Tottenham ta.

A ranar Talata ne United da ke rike da kofin Europa za ta kara a gasar Super Cup na Uefa, da Madrid,wadda ta dauki kofin Zakarun Turai.

Tsohon kociyan na Real ya ce idan har Bale ya yi wasan to babbar alama ce da ke nuna cewa zai ci gaba da zama a can, domin yana cikin tsaretsaren Zidane kenan.

Ya ce to daga nan ba ma zai bata lokacinsa ba ya yi tunanin zawarcin dan wasan. Kociyan dan Portugal ya kara da cewa, amma in dai har aka samu sabanin haka, Bale ya kasance a kofar tafiya, to shi kuwa zai kasance a kofar domin karbarsa.

A karshen kakar da ta wuce ne, a watan Oktoba, Bale ya sabunta kwantiraginsa a Bernabeu har zuwa shekara ta 2022, yana mai cewa yana farin cikin ci gaba da kasance da zakarun na Turai sau 12.

Tsohon dan wasan na Tottehma ya dauki kofin zakarun Turai uku a sheaku hudu da ya yi a kungiyar, kuma ya taimaka musu suka dauki La Liga na farko tun 2012.