Super Cup: Karon Manchester United da Real Madrid

Cristiano Ronaldo da abokan wasansa a lokacin atisaye Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Asabar Cristiano Ronaldo ya dawo atisaye a karon farko

A ranar Talatar nan ne za a fafata wasan cin kofin zakaran zakaru na Turai, Super Cup, tsakanin Manchester United da ta dauki kofin Europa, da Real Madrid wadda ta dauki Champions League, a babban birnin Macedonia, Skopje.

Idan United ta yi nasara, zai kasance na biyu kenan da ta dauka, bayan na 1991, lokacin da a gidanta Old Trafford ta doke Red Star Belgrade 1-0.

Kungiyar za kuma ta kasance ta biyu a kungiyoyin Ingila bayan Liverpool mai guda uku, da ta dauki kofin na Super Cup fiye da daya.

Jose Mourinho ya yi rashin nasara a karawa biyu ta baya a gasar, a matsayin kociya, farko a 2013 yana tare da Chelsea da kuma 2003 lokacin yana horad da FC Porto. Babu wani kociya da ya taba rashin nasarar daukar kofin sau uku.

Kuma kociyan ya kasance na farko da ya jagoranci kungiyoyi uku a gasar ta Super Cup.

Kungiyoyin Spaniya ne suka dauki bakwai daga cikin kofin guda takwas da aka fafata a kansu.

Kungiyar karshe da ta dauki kofin Europa, kuma ta yi nasarar cin kofin na Super Cup, ita ce Atletico Madrid a 2012, lokacin da ta doke, Chelsea wadda ta dauki Champions League 4-1.

Barcelona ce kawai da AC Milan kofi biyar, suka fi Real Madrid cin kofin, inda take da uku.

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin a gasar Turai da cin kwallo 108, da suka hada da biyu a gasar cin kofin na Super Cup.