Abubuwan da suka faru a Premier bayan shekara 25

Sir Alex Ferguson da Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Sir Alex Ferguson da Cristiano Ronaldo a Manchester United

Yayin da ake shirin fara gasar Premier ta bana a karshen makon nan, gasar ta cika shekara 25 da aka bullo da ita, kuma idan aka duba tsawon wannan lokaci an samu sauye-sauye kan yadda take a da, ga kuma tarin abubuwan da suka faru a ciki zuwa yanzu.

Gasar Premier yadda take a yau ta bambanta da yadda take a da, lokacin da ta faro da kungiyoyin kwallon kafa irin su Oldham da Athletic da Wimbledon.

A tsawon wannan wannan tafiya ta shekara 25, an yi wasa 9,746, yayin da aka zura kwallo 25,769 a raga, a tsakanin kungiyoyi 47.

Haka kuma an ba wa 'yan wasa jan kati, wato na kora daga fili har guda 1,477 a tarihin gasar ta Premier.

Gasar Premier na cike da matsaloli da sallamar koci-koci na kungiyoyi a wannan lokacin, ba kamar yadda take ba a 1992.

Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Sir Alex da Mourinho

A kakar farko ta gasar kociya daya kawai aka kora Ian Porterfield na Chelsea bayan wasa 29 daga cikin 42, ranar 15 ga watan Fabrairu na 1993. Daga nan kuma abin sai karuwa yake a kai a kai ba kakkautawa.

A tsakanin watan Agusta na 1994 da Agustan 1995, kungiyoyi 15 sun sauya kociyansu, inda guda takwas suka kori nasu daga aiki.

Bayan kaka uku ana wasa 42 a tsakanin kungiyoyi 22, gasar ta Ingila wadda tuni ta samu makudan kudade daga nuna wasanninta ta talabijin, an rage ta zuwa tsarin wasa 38 tsakanin kungiyoyi 20.

Yawan Cin Kwallo

Babu kungiyar da ta fi Manchester United cin kwallo a gasar Premier, inda ta zura 1,856, ta zarta Arsenal mai bi mata a matsayi na biyu da kwallo 158.

A kakar farko ta gasar ta 92-93 an zura jumullar kwallo 1,222 - Brian Deane na Sheffield United ne ya fara daga raga, lokacin da ya ci Manchester United da ka, bayan minti biyar da shiga fili a Bramall Lane.

Yawan 'Yan kallo

A shekara 25 da ta wuce samun tikiti ko shiga kallon wasan Premier ba wata wahala ba ce, amma a yanzu abin ba haka yake ba.

'Yan kallo 12,681 suka shiga wasan tsohon filin Coventry, Highfield Road ranar 15 ga watan Agusta na 1992 lokacin da Sky Blues din ta doke Middlesbrough 2-1.

Yayin da Arsenal da Chelsea suka kasa samun 'yan kallo 25,000 a wasansu na gida na farkon bude gasar, a wancan lokacin.

Sannan mutane 3,039 ne kawai suka halarci wasan da Tony Cottee ya ci wa Everton kwallo biyu, lokacin da ta doke Wimbledon 3-1 a Selhurst Park ranar 26 ga watan Janairun 1993, wanda hakan shi ne mafi karancin 'yan kallo a tarihin Premier.

Image caption Wasu alkaluma na 'yan wasa da koci-koci na Premier

'Yan kallo kasa da miliyan 10 ne ke zuwa kallon wasa 462 a kakar farko ta 1992-93, yayin da mafi yawan 'yan kallon wasan Chelsea ba sa wuce 19,000.

A kakar 2016-17, 'yan kallo miliyan 13 da dubu dari shida ne suka kalli wasa 380, inda daya bisa hudu na kungiyoyin kowacce ta samu 'yan kallo sama da 50,000 - Manchester United (75,290), Arsenal (59,957), West Ham (56,972), Manchester City (54,019) da kuma Liverpool (53,016).

A cikin shekara 25 din da ta wuce kungiyoyi da dama da suka hada da Manchester United da Chelsea da kuma Liverpool, sun kara girman filinsu, yayin da wasu kamar Arsenal da Manchester City da Southampton suka yi sabbi.

Idan ka hada alkaluman yawan 'yan kallon kowanne daga cikin wasa 9,746 za ka ga sun wuce sama da miliyan 313, wanda yawan al'ummar Amurka a 2010 miliyan 308 ne kawai.