Cutar amai da gudawa ta kama 'yan wasa a Landan

'yan tseren Jamaica da Botswana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan tseren Jamaica Gaye da na Botswana Makwalala

Wata cuta ta amai da gudawa ta kama 'yan gasar duniya ta tsalle-tsalle da guje-guje da ke zaune a wani otal a birnin Landan inda ake yin gasar.

Hukumomin lafiya na Ingila sun ce kawo yanzu 'yan wasa 30 da wasu jami'ai sun kamu da alamun cutar, kuma an tabbatar da hakan a kan guda biyu.

Duk da ficewa da ya yi daga gasar tseren mita 200 ta karshe, ranar Litinin bayan da ya kamu har ya yi amai, gwarzon dan tseren Botswana na mita 400 Isaac Makwala ya ce zai yi tseren karshe na mita 400, a Talatar nan.

A makon da ya gabata ne 'yan wasan Jamus da Canada da ke da masauki a otal din Tower Hotel suka kamu da rashin lafiya.

Saboda haka ne wata tawagar 'yan wasan Jamus mai mutane 30 za ta sauka a wasu otal otal din daban da wancan, yayin da aka dukufa domin shawo kan matsalar.

Hukumomin otal din da aka samu cutar, Tower Hotel sun ce binciken da aka yi da jami'an lafiyar muhalli tare da na hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ya nuna cewa ba a otal din ba ne cutar ta samo asali.