Ana kiki-kaka kan tafiyar Coutinho Barcelona

Jurgen Klopp rungume da Philippe Coutinho
Bayanan hoto,

Jurgen Klopp ba ya son rabuwa da Philippe Coutinho

'Yan sa'o'i kadan suka rage kafin Barcelona ta dauke gwanin dan wasan Liverpool na Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 25, bayan da wakilan kungiyar ta Spaniya suka tashi takanas ta Kano suka tafi Liverpool a ranar Talata domin a yi ta ta kare a cinikin.

Jaridar Sport ta ruwaito wannan labari ne daga Metro, yayin da kuma ake samun wasu rahotannin da ke nuna cewa abu ne mai wuya tafiyar dan wasan ta tabbata saboda kociyansa yana sonsa.

Amma kuma jaridar the Sun ta kara da cewa dan wasan tsakiya na Portugal Andre Gomes kila ya je Liverpool din a karkashin yarjejeniyar cinikin Coutinho din.

Sai dai yayin da duk ake wannan magana kociyan Liverpool Jurgen Klop jaridar Daily Mirror ta ruwaito cewa kociyan dan jamus zai yi tsayuwar daka kan hana dan wasan tafiya Barcelona.

Yayin da shi kuma tsohon dan wasan Liverpool din Graeme Souness aka jiyo shi yana cewa kungiyar ba za ta iya rike Coutinho din ba a yanzu, in ji Sky Sports.

Shi ma dai tsohon dan wasan gaba na Ingila Ian Wright, cewa ya yi ai dole ne ma Coutinho ya tafi Barcelona.

Ita kuwa kungiyar Chelsea tana sa ran karin sabbin 'yan wasa kusan hudu ne kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan ta yanzu, inda dan wasan Leicester City Danny Drinkwater, mai shekara 27, ke gaba-gaba a jerin sunayen wadanda kociya Conte ke hari.