Watford ta sayi matashin Brazil Richarlison

Richarlison (daga hagu) Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rahotanni sun ce Chelsea ma ta so sayen Richarlison (na hagu)

Watford ta tabbatar da sayen matashin dan wasan Brazil na tawagar 'yan kasa da shekara 20 Richarlison, bayan da ya samu takardar izinin aiki a Ingila.

Dan wasan na gaba mai shekara 20 ya kulla kwantiragin shekara biyar ne daga Fluminense a kan kudi fam miliyan 11.

Fluminense da ke rukuni na daya a Brazil ta dauko Richarlison ne daga kungiyar America Mineiro da ke rukuni na biyu a kasar,a shekarar da ta wuce ta 2016.

Ya yi wa Fluminense wasa 67, inda ya ci mata kwallo 19, yayin da ya ci wa tawagar Brazil ta 'yan kasa da shekara 20, kwallo biyu a wasa takwas.

Watford za ta fara wasanta na Premier ne a gida da Liverpool ranar Asabar da karfe12:30 na rana agogon Najeriya da Nijar.