Real Madrid ta dauki kofi bayan doke Man United 2-1

Isco na murnar cin kwallo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Isco ya ci kwallo 10 a 2017 a dukkanin wasannin da ya yi wa Real Madrid fiye da duk wani dan tsakiya na La Liga

Real Madrid ta sake rike kofin zakaran zakaru na Turai, Super Cup, bayan da ta doke Manchester United da ci 2-1 a wasan da ta mamaye su a babban birnin Macedonia, Skopje, cikin tsananin zafi.

Casemiro ne ya fara daga raga a minti na 24 bayan da Dani Carvajal ya sako kwallo tsakanin 'yan bayan United din.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 52 sai Isco, ya tura wa Gareth Bale kwallo, shi ma ya mayar masa, a wani ba-ni-in-ba-ka suka yi, dan Spaniyar ya sheka ta biyu a raga.

Romelu Lukaku, wanda ya barar da wata dama, bayan golan Madrid ya yi aman harin da Pogba ya kai da ka can a minti na 54, bayan minti bakwai tsakani ya natsu ya sheka daya a raga bayan wani aman da Keylor Navas din ya sake yi.

Idan dai ba a manta ba kwana 16 da ya wuce kungiyoyin biyu suka kara a Santa Clara, Amurka, inda suka tashi 11, amma kuma United ta yi nasara a bugun fanareti.

Jose Mourinho bai taba doke Real Madrid a wata gasa ba, inda ya yi canjaras daya, ya yi rashin nasara sau hudu a karawa biyar.