Neymar ka iya sake jinkirta taka leda a Paris St-Germain

Neymar PSG Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Neymar zai karbi albashin Fam 782,000 (kimanin naira miliyan 317 ) a ko wane wata a yarjejeniyarsa ta shekara biyar a PSG

Wasan Neymar na farko a Paris St-Germain ka iya sake samun jinkiri saboda har yanzu hukumomin kwallon kafa a Faransa ba su samu takardun amincewa da cinikinsa ba, bayan ya kafa tarihin koma wa PSG daga Barcelona a kan fam miliyan 200.

Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta ba wa takwararta ta Spaniya wa'adin zuwa daren Alhamis domin aika mata takardun amincewa da komwarsa kungiyar PSG a gasar Ligue 1.

Kuma matukar wa'adin ya wuce, Neymar ba zai buga wa PSG wasa a Guingamp ranar Lahadi ba.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba