Kun san hobbasar da Usain Bolt ya yi a tarihin wasanni?

Usain Bolt

Shakka babu Usain Bolt shi ne dan tseren da ya fi ko wanne a tarihi.

A dadidai lokacin da dan asalin Jamaican ke kokarin daf da yin ritaya wato bayan kammala gasar tseren duniya da ke gudanar a Landan, mun duba dalilai 9.58 da ya kamata a ce masa mashahurin dan wasa da kuma yadda ya cimma wannan matsayi.

1

Shi ne dan wasan tseren da ya fi kowa gudu a tarihi. Ya kafa tarihi ne a baya-bayan nan sau uku a tseren mita 100, kuma shekara tara ke nan tun da ya fara kafa tarihin.

The 100m world record has fallen from 10.6 seconds in 1912 to 9.58 seconds in 2009.

Bolt ya zarce tarihin da takwararsa na Jamaica, Asafa Powell, ya kafa na kammala tseren cikin dakika 9.74 ta hanyar kammalawa a cikin dakika 9.72 a watan Mayun shekarar 2008, sannan ya kara rage dakikun zuwa dakika 9.69 a gasar Olympics da aka yi a birnin Beijing a bara.

A gasar tseren duniya da aka yi a shekarar 2009 a birnin Berlin, ya sake kafa tarihi, inda ya kammala tseren cikin dakika 9.58.

A shekarar 1912, dan kasar Amurka, Donald Lippincott, ya kammala tseren cikin dakika 10.6 a birnin Stockholm inda ya kafa tarihin da sabuwar hukumar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya (IAAF) ta martaba shi.

Jim Hines, a shekarar 1968, ya kasance mutum na farko da ya fara kammala tseren cikin kasa da dakika 10, amman an kai kusan karni daya kafin Bolt ya zo ya kammala tseren cikin kasa da dakika 1 cur akan tarhin da Lippincott ya kafa.

2

Sau da yawa dai yakan kara gudu ne.Cikin jerin sunayen wadanda suka kammala tseren mita 100 cikin kasa da dakika 10 da hukumar IAAF ta fitar kafin tseren Landan, kadan ne cikin abokan gogayya da suka zo kusa da lokacin da Bolt ya karasa tserensa.

Scatterplot chart of every 100m run under 10 seconds

Tun lokacin da Hines ya kafa tarihi, wasu mutane 124 sun kammala tseren mita 100 cikin kasa da dakika 10.

Sai dai babu wani face Bolt da takwarorinsa na Jamaican Yohan Blake da Asafa Powell, da kuma Amurkawa Justin Gatlin da Tyson Gay (da aka ayyana cikin taswirar da ke kasa) da ya kammala tseren cikin kasa da dakika 9.78.

Bolt da kansa ya cimma wannan sau tara - wato fiye da kowa.

3

Ba tseren mita 100 ba ne kawai. Bolt ya yi nasara a tseren mita 200 kuma shi kadai ne ya kafa tarihi a tseren mita 100 da na mita 200 tun lokacin da hukumar IAAF ta fara amfani da na'urar auna lokaci mai sarrafa kansa a shekarar 1977.

A gasar Olympics da aka yi a Beijing a shekarar 2008, Bolt ya zarce tarihin da dan tseren Amurka, Michael Johnson ya kafa shekara 12 kafin wanna lokacin a tseren mita 200, inda Bolt ya zarce tarhin kammala tseren cikin dakika 19.32 ta hanyar kammala tseren cikin dakika 19.30 kafin daga bisani ya zarce lokacin ta hanyar kammala tseren cikin dakika 19.19 bayan shekara daya a birnin Berlin.

4

Ci gabansa da taka rawargani mai ban mamaki. Banda gasar da aka yi a Landan a shekarar 2017, Bolt ya yi nasara a kusan ko wacce gasar Olympics da ta tseren duniya da ya shiga tun shekarar 2008 .

A gasar da ka yi a birnin Rio cikin shekarar 2016, Bolt ya ci lambar yabo uku a jere a tseren mita 100 da na mita 200 da kuma tseren mika sanda na mita 100, abin da, a cewarsa, ya sa 'ya fi karfin mutuwa.'

Bolt ya riga ya rasa kambun tseren mika sanda na shekarar 2008 bayan an samu haramtaccen kwaya a jinin dan takwaransa Nesta Carter - lamarin da ya shafi dukkan 'yan tawagarsu na tseren mika sandan.

Carter dai ya daukaka kara a kotun daukaka kara ta wasanni.

Matsalolin da tarihin tseren Bolt ke da su su ne tagullar da ya samu a gasar da aka yi a Landan a shekarar 2017 da kuma fara tsere ba bisa ka'ida ba a tseren mita 100 da aka yi a Daegu a kasar Korea ta Kudu a shekarar 2011, lamarin da ya sa aka hana shi ci gaba da gasar.

5

Tun daga shekarar 2008, sau daya ne kawai ya sha kaye a tseren mita 200 - daga hannun dan uwansa dan Jamaica Blake a gasar tseren Jamaican da aka yi a shekarar 2012.

Blake ya kuma lashe tseren mita 100 a wannar gasar, wannan ne daya daga cikin lokuta biyar da Bolt ya kasa yin nasara a irin wannan tazarar a wata muhimmiyar gasa.

Gatlin da Christian Coleman da Powell da kuma Gay su ne sauran 'yan wasan tsere da suka kayar da Bolt a tseren mita 100.

6

Saurin Bolt ya wuce yadda ake tsammani. Bolt ya yi tseren mita 10 daga cikin tseren mita darinsa mafi sauri cikin dakika 0.81. Wannan ya yi daidai da gudun mil 27.66 a ko wacce sa'a, kusan iyakar gudun doki mai daka tsalle ke nan.

Amman dan Jamaican ya yi saurin kammala tseren mita 100 cikin kasa da dakika 9.58 a lokacin da aka ba shi izinin fara gudu yana sassarfa.

Ya yi rabin karshe na dakikansa 19.19 a tseren mita 200 cikin dakika 9.26 kuma ya yi gudu da kyau cikin kasa da dakiku tara a tseren mika sanda na mita 100, inda ya fi sauri a lokacin da ya kammala tseren cikin dakika 8.65 a shekarar 2015.

Amman shekaru da ciwo sun yi tasiri kan Bolt wanda a yanzu yake da shekara 31 da haihuwa.

Saurinsa a kaka a ya ragu kuma ya rage yawan tseren da yake shiga.

A shekarar 2016 ya yi gudu mita 100 cikin dakika 9.81 da kuma gudun mita 200 cikin dakika 19.78, wannan bai yi sauri ba in aka yi la'akari da yadda ya saba yi, amman lokutan sun sa ya yi nasara duk da hakan.

7

Ta yaya yake yi? Babu wata amsa mai sauki ga wannan tambayar, amman wani binciken da Mackala Krzysztof da Antti Mero suka gudar kuma aka buga mujallar da ake kira Journal of Human Kinetics, sun gano cewa tsawonshi na kafa shida da inci biyar (Sentimita 195) na daga cikin dalilan da ke daura shi gaban masu gogayya da shi.

Ana yawan ganin tsawo a matsayin wata illa ga masu tsere a lokacin da za a fara tsere domin yana iya rage karfi a lokacin da suka turo gaba a kwance domin su samu karfin gudu.

Amman, binciken ya ce, a tsakiyar tsere"tsawon jikin Bolt yakan sa ya iya ci gaba da dan karen gudu cikin wani lokaci mafi tsawo ya kuma rage gudu kadan-kadan fiye da masu tseren da ba su kai shi tsawo ba."

8Tsawon ko wanne takunsa ka iya kai mita 2.47.

Wannan ya zarce na yawancin masu gogayya da shi da Santimita 20 - amman yana tabbatar da yawan taku.

Wadannan abubuwa suna daura shi a kan abokan gogayyarsa saboda haka in har Bolt ya fara dugu, zai iya yin zarra da ko wane taku.

Dan tseren dan asalin kasar Jamaica ya kammala tserensa na kafa tarihi a tseren mita 100 cikin kasa da dakika 41, a lokacin da sauran wadanda suka kai tseren karshen sun kammala a cikin matsakaicin lokacin da ya kai dakika 45, in ji binciken Krzysztof da Mero.

9 Amman yaya ake yi da jinkirin da 'yan tsere da ke da tsawo ke yi?

Bolt yana shawo kan matsalar ne -a yawancin lokuta.

Da gaske ya fi jinkiri da farkon tsere a kan sauran masu gogayya da shi: ida ka dubi dukkan martanin da yake mayarwa a gasarsa na Olympic da gasar duniya a matakin mita 100 (Afec inda ya fara tsere kafin a ba da izini a gasar da aka yi a Daegu a shekarar 2011).

Amman, in ji Michael Johnson, a tseren shi mafi kyau, Bolt na iya irin sa jiki na wadanda ba su kai shi tsawo ba.

Johnson ya shaida wa Olympic Channel cewa: "Za ka ga cewa a mita 30 na farko ko makamancin haka yana nan tare da da wadanda suka fi shi gajarta, abin da ba kasafai ake ganin irinsa ba."

A tarhin tseren da ya kafa, Bolt ne ya fi kowa sauri.

A lokacin da aka kai mita 20 za ka yana kan gaba, kuma ya fi kowa sauri dukkan wani mita 20 na gaba.

A gasar da aka yi a Landan a shekarar 2017, duk da cewa lokacin mayar da martaninsa na dakika 0.183 ya yi masa jinkiri - kuma yana bayan kowa da dakika 0.031 a tseren.

9.58

Ga Bolt, akwai abubuwa a ko da yaushe bayan tsere.

Tun daga tsayuwarsa 'Bolt walkiya' zuwa watangaririyarsa a cikin filin wasa da kuma ikirarinsa na cin 'kimanin soyayyen naman kaji 1,000a gasar Olympics da aka yi a Beijin, kasancewar Bolt mai wasa da jama'a ya sa ya zama fitaccen tauraro.

Sukar da ake masa lokaci-lokaci kan cewa yana nuna kansa kafin ya wuce layin karshen tsere bai yi wani mummunan tasiri kan sunansa ba.

A ranar jajiberin murabus dinsa ya kasance daya daga cikin 'yan tsere da aka fi sani a shafukan sada zumunta inda mutum miliyan 19 ke binsa a Facebook, kuma miliyan 7.1 ke binsa a Instagram kuma mutum miliyan 4.75 ke binsa a Twitter.

Tare da sunansa ne tallafi ke zuwa.

Yarjejeniyoyinsa da kamfanonin Puma da Mumm champagne da Advil da sauransu sun sa kudin da yake samu a ko wace shekara ya kai fam miliyan 26.2 a shekarar 2016 zuwa 2017, in ji mujallar Forbes wadda ta saka shi a mataki na 88 a jerin sunayen taurari 100 da ta yi. da suka fi arziki.

Bolt yana ba kungiyoyin agaji ta gidauniyarsa tare da tallafin shekaru ga tsohuwar makarantarsa ta sakandare a unguwar Trelawny da ke Jamaica.

Amma anya mutane za su iya mantawa da Bolt a nan kusa?

Bayan ga haka, mai yiwuwa ne zai ci gaba da taka rawa a fagen tsere na duniya.

Amman ba bu shakka cewa wasan zai yi kewarshi.

Shugaban hukumar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya (IAAF), Lord Coe ya shaida wa BBC: "Abin da za mu yi kewa shi ne kasancewarsa fitaccen dan tsere. Muna son 'yan wasan tsere fitattu."