Kwallon Golf : McIlroy ya ce ba ya bukatar wata bajinta

Rory McIlroy a lokacin atisayen gasar Amurka ta US PGA Championship Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rory McIlroy ya ce ba shi da wata gwaninta da yake son nuna wa kuma

Rory McIlroy ya ce ba shi da sauran wata bajinta da yake bukatar ya nuna yayin da yake kokarin cin babban kofinsa na farko a shekara uku a gasar kwallon golf ta Amurka.

Gwanin kwallon lambun na hudu a duniya, yana daga cikin mutum hudu da ake ganin za su yi nasara a gasar, wadda ake yi a filin Quail Hollow, inda ya yi nasara sau biyu da kuma tarihin bajintar da aka taba yi a filin.

McIlroy ya ce : "ba zan matsa wa kaina ba ta cewa sai na yi wata bajinta. Na riga na nuna wa duniya kokarina a cikin shekara tara da ta wuce,'' In ji shi.

Dan Ireland ta Arewar ya kara da cewa, ''ban taba karaya ba. A ko da yaushe na yarda da kaina. Kuma har yanzu haka nake.''

Maganar ta gwanin wanda sau hudu yana daukar babban kofi na kwallon golf din, ta saba da yadda yake a 2015, lokacin da ya karya bajintar da ya taba kafawa, kafin ya dauki kofi a lokacin yana na daya a duniya, wanda a lokacin ya ce yana son ya nuna wa duniya gwanintarsa.

McIlroy mai shekara 28, ya ce a wannan makon ba ya son a sa shi a gaba ya yi wata magana ko kuma ya yi wani abu da zai nuna wa wani mutum, shi shi ne, ya ce ya wuce wannan matsayin.