Gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta London

Mo Farah ya ci zinare a gasar gudun mita 10,000
Image caption Farah ya ci lambar zinare a gasar gudun mita 10,000 ta duniya a karo na uku a jere

Ba'amurkiya Allyson Felix na harin cin lambar bajintarta ta duniya ta goma a shirin da take yi na shiga tseren mita 400 na karshe a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da ake yi a Landan, ranar Larabar nan.

'Yar kasar Bahama Shaunae Miller-Uibo da 'yar Bahrain Salwa Eid Naser su ne babbar barazanarta a gasar.

Shi kuwa dan Birtaniya Mo Farah, wanda zai koma gasar gudu a titi, ya bar ta filin wasa a kaka ta gaba, ya fara gasarsa ta bankwana da lamabra zinare da ya ci a gudun mita 10,000, kuma zai fara shirin fafatawa a gasar mita 5,000.

Gwarzo dan Jamaica Usain Bolt, wanda ya ci lambar tagulla bayan da ya zo na uku a gasar tseren mita 100, na shirin kawo karshen wasansa da ya cimma gagarumar nasara a duniya, ta hanyar cin lambar zinare a tseren karba-karba na mutum hudu na mita 100, wanda za a yi ranar Asabar.

Lambobin zinare 48 ne dai za a ci a gasar ta guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta kwana goma ta wannan shekara ta 2017, da ake yi a Landan.

Shekara biyu da ta wuce Birtaniya ta ci lambobinta na zinare hudu a karon farko a gasar ta duniya, ta hannun Mo Farah, wanda ya ci biyu, da Jessica Ennis-Hill da kuma Greg Rutherford.

Wannan nasara ta ba wa Birtaniya damar kammala gasar a wancan lokacin a matsayi na hudu, bayan Kenya da Jamaica da kuma Amurka, wadda ta kasance ta daya.