Ina son barin Liverpool – Philippe Coutinho

Philippe Coutinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Philippe Coutinho ya ci kwallo 13 a wasa 31 na Gasar Firimiya da ya buga wa Liverpool bara

Dan wasan Liverpool Philippe Coutinho ya bayyana bukatar barin kungiyar, bayan kulob din ya fitar da wata sanarwa wadda a ciki ya ce dan wasan ba na sayarwa ba ne.

Coutinho ya bayyana aniyyarsa ta barin kungiyar ce a wata wasikar e-mail. Sai dai kungiyar ta yi watsi da bukatarsa.

Liverpool dai ta ce dan wasan tsakiyarta na kasar Brazil Philippe Coutinho "tabbas" ba na sayarwa ne.

A ranar Laraba ce, kungiyar ta ce a kai kasuwa ga tayin yuro miliyan 100 da Barcelona sake yi wa dan wasan mai shekara 25.

Tayin Barca na farko, wanda nan take Liverpool ta ce albarka, ya kunshi biyan kusan yuro miliyan 77, da karin yuro miliyan 13 da rabi a kai.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, masu mallakar kungiyar, Fenway Sports Group, sun ce, "matsayin tsayin dakan" da suka yi, shi ne "babu wani tayi da zai ja hankalinmu".

Liverpool ta kara da cewa: "Philippe zai ci gaba da zama a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool har bayan rufe kasuwar 'yan wasa ta bazara."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Da yake jawabi a wani taron manema labarai gabanin fara karawa ranar Asabar a gasar Firimiyar Ingila a Watford, kocin kungiyar Jurgen Klopp ya ce Coutinho ba zai buga wasan Liverpool na farko ba saboda matsalar ciwon baya.

Klopp ya kuma bayyana tantama kan bayyanarsa a wasan samun cancantar shiga Gasar Zakarun Turai zagayen farko da Liverpool za ta yi ranar Talata a Hoffenheim don kuwa Coutinho "bai yi atisaye ba tun ranar Juma'a a makon jiya".

Coutinho, wanda ya ci kwallo 14 a dukkan gasannin da ya buga a kakar da ta wuce, ya sa hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar shekara biyar a watan Janairu, wadda ba ta kunshi shadarar fitarsa ba. A shekara ta 2013 ne dan wasan ya shiga Liverpool a kan yuro miliyan 8 da rabi daga Inter Milan.

Haka zalika, an ki sallama wa Barcelona tayin da ta yi wa dan wasan gaba na Borussia Dortmund Ousmane Dembele, tun bayan sayar da dan wasan gaba na Brazil Neymar a kan kudi mafi tsada na yuro miliyan 200 ga Paris St-Germain cikin makon jiya.