Nigeria: Yadda za ku amfana da shirin tallafin gwamnati na YouWin

YouWin Hakkin mallakar hoto Facebook/YouWin
Image caption Tshon shirin YouWin dai ya taimaka wa matasa wajen fara sana'o'i

A shekarar 2011 ne gwamnatin Najeriya ta fito da shirin YouWin, inda ta tallafa wa matasa masu shirin fara sana'o'in kansu ta hanyar ba su kudi da kuma shawarwarin yadda za su bunkasa abin da suka sanya a gaba.

Kimanin shekaru biyu bayan an dakatar da shirin, sai gwamnatin kasar ta sake bullowa da shirin amman da sabon suna - wato YouWIN! Connect, domin a cewar ma'aikatar kudin kasar, wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin a karon farko ba su kai labari ba domin rashin kwarewa kan yadda ake tafiyar da kasuwanci.

Saboda haka an bullo da shirin ne domin magance matsalar da aka fuskanta a tsohon shirin da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa tare da magance matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa.

Su waye za su iya amfana daga shirin?

Kafin mutum ya cancanci cin gajiyar shirin sai ya cika sharruda takwas ciki har da kasancewa dan Najeriya mai zama cikin kasar, kuma wanda ya kai matakin karatun gaba da sakandare.

Har ila yau, wajibi ne mutum ya kasance yana tsakanin shekara 18 zuwa 40, ya iya magana da Ingilishi kuma ya kasance yana sana'arsa a cikin Najeriya.

Baya ga haka ana bukatar mutum ya kasance ba ma'aikacin gwamanti ba ne, har ila yau, ya kasance wanda bai taba cin gajiyar shirin ba.

Hakazalika ana son mutum ya yarda cewa zai halarci duka wata horarwa da kuma bibiyar da shirin zai yi.

Idan mutum ya cika wadannan sharuddan, yana da damar cin gajiyar shirin, kamar yadda ma'aikatar kudin kasar ta bayyana.

Wadannan sharrudan suna nuna cewa wanda ya kammala karatu a matakin difloma ko NCE na iya amfana da shirin.

Har ila yau sharuddan sun nuna cewa mazauna karkara ma za su iya cin gajiyar shirin.

  • Ga Malam Salisu Na'inna Danbatta da karin bayani game da yadda za a amfana da shirin, sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraro.
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda za a ci gajiyar shirin YouWin, in ji ma'akatar kudi Najeriya

Yadda ake shiga shirin

Duk mai son shiga shirin zai fara ziyartan shafin Intanet ne na www.youwinconnect.org.ng inda zai samu karin bayani game yadda zai yi rijista.

Amman yin rijista mataki na farko ne kawai cikin matakai biyar da mutum zai bi wajen cin gajiyar shirin.

Rijista da ware mutane

Bayan wadanda suke son cin gajiyar shirin sun yi rijista, sai a ware mutum 55,000 daga cikin wadanda suka yi rijista.

Horarwar Intanet

Bayan haka sai a ba mutum 55,500 da aka ware horo ta Intanet kan bangarori daban-daban na sana'a da kasuwanci kamar yadda ake shirya tafiyar da kasuwanci (samun kudi da samun abokan ciniki da yin zarra a kasuwa da dabaran kasuwanci da kuma sauya tunani).

A karshen wannan matakin, za a ware mutum 5,000 da suka yi nasara domin su samu horarwa ta musamman domin kwarewa.

Kuma za a gudanar da horarwar ce ido-da-ido.

Horarwar Ido-da-ido

A horarwa ta kwarewar da mutum 5,000 za su samu koyarwa (bisa ga fanin da ko wanne ke so).

Ita horarwar an raba ta kashi-kashi dangane da cibiyoyin koyarwar da ke fadin kasar.

Fannonnin da za a mayar da hankali a horarwar kwarewar sun hada:

•Fasahar yada labarai da sadarwa (ICT)

•Noma da sarrafa amfanin gona

•Dinki

•Masana'antu da sayar da kasuwanci

•Gine-gine

Dukkan wadanda suka halarci horon za su samu takardun shaida na kammala horarwar kuma za a bukace su da su mika takardar tsarin kasuwanci saboda a ga inda kasuwancinsu ke bukatar shawara ko gyara.

Tallafin bunkasa sana'a

Dukkan masu sana'ar da suka samu aka tallafa musu da kudi za su samu tallafin bunkasa sana'a na tsawon shekara daya (Wannan ya hada da hada masana'antu da cibiyoyin ba da agaji domin karin kudi).

Labarai masu alaka