Ko Hazard zai koma Madrid?

Harzard Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hazard ya koma Chelsea a shekarar 2012 daga kulob din Lille na kasar Faransa

Kungiyar Real Madrid ta dakatar da neman Mbappe, kuma wata kila ta fara zawarcin dan wasan Chelsea, Eden Hazard, kamar yadda jaridar Daily Star ta wallafa.

Kungiyar Barcelona ta mayar da hankalinta ga zawarcin dan wasan Tottenham, Christian Eriksen, saboda Liverpool ta ki sayar mata da Philippe Coutinho, in ji jaridar Independent.

Liverpool ta yankawa Coutinho farashin fam miliyan 136.5 yayin da ake cinikinsa a wannan mako, kamar yadda jaridar Daily Record ta bayyana.

Har ila yau, Barcelona ta ci gaba da neman dan wasan Borussia Dortmund, Ousmane Dembele, inda yanzu ta nemi ta biya fam miliyan 140 don mallakarsa, in ji AS.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dembele mai shekara 20 ya koma Borussia Dortmund daga kungiyar Rennes a shekarar 2016

Jaridar Sport Italia cewa ta yi idan Barcelona ta rasa Dembele da Coutinho, to za ta nemi Ivan Perisic na Inter Milan ne wanda Manchester United take zawarcinsa.

Hakazalika, dan wasan tsakiyar Paris St-Germain (PSG), Angel di Maria, zai iya kasancewa wanda zai maye gurbin Neymar din, kamar yadda jaridar Sport ta ce.

PSG ta yi tayin biyan Kylian Mbappe albashin fam miliyan 16.4 a yarjejeniyar shekara biyar don ya amince ya bar Monaco, a cewar jaridar L'Equipe ta kasar Faransa.

Mbappe ya kagu ya koma PSG amma da wuya hakarsa ta cimma ruwa a kakar bana, in ji kafar yada labarai ta ESPN.

Chelsea ta ki kara wani abu a kan tayin da ta yi wa dan wasan Leicester City, Danny Drinkwater, wanda aka ki sallama mata shi a kan fam miliyan 15, in ji jaridar Telegraph.

Labarai masu alaka