Neymar zai yi wa PSG wasa ranar Lahadi

PSG Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Neymar ne dan kwallon da aka saya mafi tsada a duniya a bana

Dan kwallon tawagar Brazil, Neymar zai buga wa Paris St-Germain wasan farko a gasar Faransa a ranar Lahadi.

Hukumar da ke gudanar da gasar Faransa ce ta samu tabbacin kammala cinikin Neymar kan fam miliyan 200 daga Barcelona.

Saboda haka dan kwallon mai shekara 25, zai yi wa PSG wasansa na farko a karawar da za ta ziyarci Guingamp a ranar ta Lahadi a makon farko a Ligue 1.

Kocin PSG, Unai Emery ne ya tabbatar da cewar Neymar yana cikin koshin lafiya ya kuma shirya buga wa kungiyar tamaula.

Neymar ya koma PSG daga Barcelona a makon jiya, sai dai ya gamu da tsaiko, bayan da hukumar kwallon Spaniya ba ta bayar da takardun amincewa ya koma Faransa da taka-leda da wuri ba.

Labarai masu alaka