Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid

El Clasico Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ce ta doke Real Madrid a International Champions Cup a Amurka da ci 3-2

Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan hamayya da ake kira El-Clasico a ranar Lahadi a Nou Camp.

Kungiyoyin biyu za su kara ne a Spanish Super Cup wasan farko, wanda Barcelona za ta karbi bakunci.

A kuma rana 16 ga watan Agusta za a buga wasa na biyu, inda Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a Santiago Bernabeu.

Za a buga Spanish Super Cup ne tsakanin Real Madrid wadda ta lashe La Liga da aka kare da Barcelona mai Copa del Rey.

A watan jiya ne Real da Barca suka buga El-Clasico a filin wasa na Hard Rock da ke Miami a birnin Floridan Amurka, inda Barcelona ta yi nasara.

Haka kuma kungiyoyin za su kara a La Ligar bana, inda Barcelona za ta fara ziyartar Bernabeu a ranar Laraba 20 ga watan Disamba a wasan mako na 17 a gasar.

Sai dai kuma watakila a sauya ranar fafatawar domin Real za ta buga gasar kofin zakarun kungiyoyin nahiyar duniya, domin za a yi wasan karshe a ranar 16 ga watan Disamba.

Ita kuwa Real za ta je Camp Nou a ranar Lahadi 6 ga watan Mayu a wasan mako na 36 a gasar ta La Liga.

Labarai masu alaka