Liverpool ta fara Premier da canjaras

Premier week 1 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool za ta karbi bakuncin Palace a ranar Asabar

Watford da Liverpool sun tashi wasa 3-3 a makon farko a gasar Premier da suka fafata a ranar Asabar.

Watford ta ci kwallo ta hannun Okaka da Doucoure da Bristos wanda ya ci biyu a karawar.

'Yan wasan Liverpool da suka ci mata kwallo sun hada da Mane da Firmino wanda ya ci a bugun fenariti da kuma wadda Salah ya ci, sabon dan wasan da ta saya a bana.

Da wannan sakamakaon kungiyoyin biyu sun raba maki dai-dai a tsakaninsu, bayan da suke da kwallaye uku-uku a raga.

Watford za ta ziyarci Bournemouth a wasan mako na biyu a ranar 19 ga watan Agusta, a kuma ranar ce Liverpool za ta karbi bakuncin Crystal Palace a Anfield.