Chelsea ta ga ta kanta a hannun Burnley

Premier week 1 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An bai wa Cahill da Fabregas jan kati a karawar da Burnley ta ci Chelsea 3-2

Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Burnley da ci 3-2 a wasan farko a gasar Premier a ranar Asabar a Stamford Bridge.

Burnley ta ci kwallo uku tun kafin a je hutu ta hannun Vokes wanda ya ci biyu a wasan sannan Ward ya kara ta uku.

Chelsea ta zare biyu ta hannun Morata bayan da aka dawo daga hutu, sannan David Luiz ya kara ta biyu saura minti biyu a tashi daga gumurzun.

Chelsea mai rike da kofin Premier ta karasa karawar da 'yan wasa tara a cikin fili, bayan da aka bai wa Cahill da Fabregas jan kati.

Wannan ne karon farko da aka ci Chelsea a wasan makon farko a gasar Premier tun bayan 1998.

Wasu sakamakon wasannin da aka yi:

  • Crystal Palace 0-3 Huddersfield
  • Everton 1-0 Stoke
  • Southampton 0-0 Swansea
  • West Brom 1-0 Bournemouth
  • Watford 3-3 Liverpool

Labarai masu alaka