An ci kwallo 25 a wasa takwas a Premier

Premier League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallaye 25 aka zura a raga a wasa takwas da aka yi a makon farko a Premier

Kwallo 25 aka zura a raga a wasa takwas da aka yi a makon farko a gasar Premier ta kakar 2017/18.

Tun a ranar Juma'a aka fara zura kwallo bakwai a raga a karawar da Arsenal ta doke Leicester City da ci 4-3 a Emirates.

Da tsakar ranar Asabar ne aka ci shida a fafatawar da aka tashi canjaras 3-3 tsakanin Watford da Liverpool.

Da yammaci kuma aka ci 11 a raga, daga ciki har da doke Chelsea 3-2 da Burnley ta yi a Stamford Bridge, wanda rabon a ci Chelsea a makon farko a Premier tun 1998.

Wasan karshe a yammacin Asabar kuwa kwallo biyu aka ci, inda Manchester City ta yi nasara a kan Brighton.

Sai a ranar Lahadi ne za a karasa sauran wasanni biyu tsakanin Newcastle United da Tottenham da fafatawa tsakanin Manchester United da West Ham United.

Ga sakamakon wasannin makon farko da aka yi:

  • Arsenal 4-3 Leicester City
  • Chelsea 2-3 Burnley
  • Crystal Palace 0-3 Huddersfield
  • Everton 1-0 Stoke
  • Southampton 0-0 Swansea
  • West Brom 1-0 Bournemouth
  • Watford 3-3 Liverpool
  • Brighton 0-2 Manchester City

Labarai masu alaka