Tottenham ta samu maki uku a Newcastle

Tottenham ta samu nasarar hada maki uku, bayan da ta doke Newcastle United har gida da ci 2-0 a wasan makon farko a gasar Premier a ranar Lahadi.
Tottenham ta fara cin kwallo ta hannun Delle Ali bayan da aka dawo daga hutu, sannan Ben Davies ya kara ta biyu.
Newcastle United wadda ta dawo buga wasannin Premier a bana ta karasa karawar da 'yan kwallo 10 a fili, bayan da aka bai wa Jonjo Shelvey jan kati.
Tottenham za ta buga wasanta na biyu a ranar Lahadi a gida da Chelsea, ita kuwa Newcastle United za ta ziyarci Huddesfield.