Man City na daf da sayen Kayode na Nigeria

Manchester City Hakkin mallakar hoto PAOLO BRUNO/GETTY IMAGES
Image caption Zai zama dan wasan City na biyar da zai koma Girona wasa aro

Manchester City na daf da kammala sayen dan Nigeria, Olarenwaju Kayode daga Vienna ta Austria kan yarjejeniyar shekara hudu.

Da zarar City ta kammala daukar dan wasan mai shekara 24 wanda ya ci kwallo 17 a fafatawa 33 da ya yi a gasar Austria, za a bayar da shi aro ga Girona ta Spaniya.

Kayode ya ci kwallo 24 a wasa 48 da ya yi wa Vienna a kakar da ta kare, ciki har da guda biyu da ya ci Roma a wasa biyu da suka kara a Europa League.

'Yan wasan City hudu ne ke buga wasa aro a sabuwar kungiya Girona wadda za ta buga La Liga da suka hada da Douglas Luiz da Pablo Maffeo da Aleix Garcia da kuma Marlos Moreno.

Labarai masu alaka