Man United ta fara tauna tsakuwa

Premier week 1 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester ta hada maki uku da kwallo hudu a wasan makon farko a Premier

Manchester United ta zazzagawa West Ham United kwallo 4-0 a wasan farko a gasar Premier da suka fafata a ranar Lahadi a Old Trafford.

United ta ci kwallo ta hannun Romelu Lukaku wanda ya ci biyu a fafatawar, sai Anthony Martial da kuma Paul Pogba da kowannensu ya ci guda-guda a raga.

Da wannan nasarar United ta yi rashin sa a sau daya kacal daga fafatawa 14 a wasan makon farko da ake bude kakar Premier.

Ita kuwa West Ham United sau 11 a jere tana rashin nasara a makon farko a gasar ta Premier.

Labarai masu alaka