Gombe United ta ci Kano Pillars 1-0

Nigerian Firimiya League Hakkin mallakar hoto LMCNPFL
Image caption Wasannin Firimiyar Nigeria na bana sun kawo gangara

Gombe United ta yi nasarar cin Kano Pillars daya mai ban haushi a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 34 da suka kara a ranar Lahadi.

Gomben ta ci kwallo ne ta hannun Ibrahim Abdullahi a bugun tazara minti shida da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Ga sakamakon wasu wasannin mako na 34:

  • Enyimba 3-0 ABS
  • Akwa 3-0 Tornadoes
  • Katsina 2-0 Wikki
  • Rangers 1-0 Sunshine Stars
  • Nasarawa 1-0 Lobi
  • Abia Warriors 2-0 3SC
  • Remo 1-3 Rivers

Labarai masu alaka