Costa ya nemi ya koma Atletico Madrid

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A shekarar 2014 Costa ya koma Chelsea da murza-leda

Diego Costa ya kwatanta abin da Chelsea ta yi masa a matsayin mai mugun laifi, ya kuma bukaci izinin komawa Athletico Madrid da taka-leda.

Dan kwallon ya ce kocin Chelsea, Antonio Conte ne ya tura masa sako ta waya, inda ya ce ba za a yi amfani da shi a wasan bana ba.

Costa mai shekara 28, ya buga wa Chelsea wasan karshe a gasar FA, wanda Arsenal ta yi nasara a watan Mayu.

Dan kwallon ya ce Chelsea ta bukaci da ya koma atisaye a cikin matasan kungiyar a yanzu haka.

'Ya kamata nayi abin da ya dace, na kasance mai halayya ta gari a Chelsea, ina kuma son yin abin da ya ce, amma yanzu burina na koma Atletico'.

Costa ya koma Chelsea daga Atletico Madrid a 2014, ya kuma ci kofin Premier biyu da League Cup a kungiyar.

Labarai masu alaka