Cristiano Ronaldo zai yi hutun dole

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ce ta doke Barcelona 3-1 a wasan farko a Nou Camp

An dakatar da Cristiano Ronaldo daga buga wasa biyar, bayan da aka ba shi jan kati a karawar da Real Madrid ta ci Barcelona 3-1 a Spanish Super Cup a ranar Lahadi.

An dakatar da Ronaldo wasa daya, bayan da aka ba shi katin gargadi biyu a Nou Camp, daya saboda ya cire rigarsa bayan da ya ci kwallo na biyu kuma ya fadi a da'ira ta 18 ta Barcelona da gangan.

An kara mai hukuncin wasa hudu saboda ya ture alkalin wasa, bayan da ya ba shi jan katin.

Ronaldo ba zai buga wasa na biyu da Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona ba.

An bai wa Ronaldo kwana 10 domin ya daukaka kara.

Dan kwallon zai buga gasar cin kofin zakarun Turai, amma ba zai buga wasannin Spaniya ba har sai ranar 20 ga watan Satumba a karawar da Madrid za ta yi da Real Betis.

Ga jerin wasannin da ba zai buga ba:

16 Agusta Barcelona a gida a gasar Spanish Super Cup

20 Agusta Deportivo La Coruna a waje a wasan La Liga

27 Agusta Valencia a gida a wasan La Liga

9 Satumba Levante a gida a wasan La Liga

17 Satumba Real Sociedad a waje a wasan La Liga

Labarai masu alaka