Barcelona za ta ziyarci Real Madrid

Spanish Super Cup Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ta ci Barcelona 3-1 a wasan farko da suka kara a ranar Lahadi a Spanish Super Cup

Barcelona za ta ziyarci Real Madrid a karawa ta biyu a Spanish Super Cup a ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Wasan farko da aka yi a a gasar a Nou Camp, Real ce ta yi nasara da cin kwallaye 3-1, kuma a karawar ce aka bai wa Cristiano jan kati.

Gerard Pique ne ya fara cin gida bayan da aka dawo daga hutu, sai Cristiano Ronaldo ya ci ta biyu sannan Marco Asensio ya ci ta uku daf da za a tashi daga wasan.

Wannan ne karo na uku da kungiyoyin za su fafata a wasan hamayya da ake yi wa kirari da sunan El Classico a bana.

Barcelona ta ci Madrid 3-2 a International Champions Cup a Amurka a wasannin atisayen tunkakar kakar bana, kuma ita ce ta lashe kofin.

Labarai masu alaka