Tevez da Shenhua sun kulla alkawari

Tevez Hakkin mallakar hoto BBC Sports
Image caption A ranar 30 ga watan Agusta Tevez zai koma China

Kungiyar Shanghai Shenhua ta amincewa Carlo Tevez ya je Argentina, amma da yarjejeniya a rubuce cewar zai koma China ranar 30 ga watan Agusta.

Akwai rahotanni da ke cewar Tevez mai shekara 33, wanda ya koma Shanghai daga Boca Junior a watan Disamba, na son barin kungiyar.

Tevez tsohon dan kwallon Manchester City ya nemi izinin zuwa Argentina domin yin maganin ciwon gwiwa da yake fama.

Dan kwallon yana daga cikin 'yan wasan da suka fi daukar albashi a fagen tamaula a duniya, inda yake karbar fam 634,615 a kowanne mako in ji jaridar The Sun.

Labarai masu alaka