Gwarzon dan kwallon Turai: Messi da Ronaldo

Messi Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo ne gwarzon dan kwallon kafa na Turai a bara

An fitar da sunayen 'yan wasa 10 da ke takarar gwarzon dan wasan tamaula da ya fi yin fice a nahiyar Turai a shekarar nan.

Cikin 'yan wasan har da mai tsaron ragar Juventus Gianluigi Buffon da Lionel Messi na Barcelona da dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo.

Masu horar da tamaula a Turai su 80 da fitattun 'yan jarida 55 ne suka fitar da 'yan wasa 10 da za a zabi wanda babu kamarsa a fagen tamaula a Turai.

Messi da Ronaldo sun lashe kyautar sau biyu kowannnensu, kuma Ronaldo ne ya lashe ta bara.

A ranar 24 ga watan Agusta za a bayyana gwarzon bana a lokacin da za a raba jadawalin gasar cin kofin zakaraun Turai ta shekarar nan da za a yi a Monaco.

Ga jerin 'yan wasa 10, bayan Buffon da Messi da kuma Ronaldo:

  • 4: Luka Modric (Croatia, Real Madrid)
  • 5: Toni Kroos (Germany, Real Madrid)
  • 6: Paulo Dybala (Argentina, Juventus)
  • 7: Sergio Ramos (Spain, Real Madrid)
  • 8: Kylian Mbappe (France, Monaco)
  • 9: Robert Lewandowski (Poland, Bayern Munich)
  • 10: Zlatan Ibrahimovic (Sweden, Manchester United)