An hana Onazi takardar buga tamaula a Ingila

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Onazi ya buga wa Nigeria gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil

An hana dan wasan tawagar kwallon kafar Nigeria, Ogenyi Onazi takardar izinin buga wa Birmingham City tamaula a Ingila.

Birmingham ta amince ta dauki dan wasan mai shekara 24 daga kungiyar Trabzonspor ta Turkiya domin ya murza-mata leda.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ki amince wa da takardar izinin buga kwallo a Ingila da Onazi ya bukata tun farko.

Haka kuma hukumar ta ki amincewa da rokon da Birmingham ta yi kan a bar dan kwallon ya taka-mata leda duk da yana buga wa Super Eagles wasa akai-akai.

Onazi ya yi wa Nigeria wasa 38, yana daga cikin 'yan kwallon da suka ci wa kasar kofin nahiyar Afirka a 2013 da taka rawa a gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil.