''Yanayin Sanchez da ban da na Diego Costa''

Image caption ''Yanayin Sanchez da ban da na Diego Costa''

Babu hadi tsakanin yanayin da Alexis Sanchez ke ciki a Arsenal da kuma na Diego Costa a Chelsea, in ji koci Arsene Wenger.

Sanchez mai shekara 28 yana shekarar karshe ta kammala kwantiraginsa a Emirates, kuma har yanzu bai amince da tsawaita zamansa a kulob din, inda shi kuma Costa ya ce yana son barin Chelsea.

Wenger mai shekara 67 ya sha fadar cewa, Sanchez yana girmama shawararsa ta ci gaba da zamansa a Arsenal a bana, duk da cewa an samu rahoton Manchester City da Paris St-Germain sun nuna sha'awarsu ta daukan dan kwallon.

A ranar Laraba ne Wenger ya ce har yanzu ba su cimma yarjejeniyar tsawaita zaman Sanchez a Arsenal ba, kuma munfi amincewa ya bar kungiyar a matsayin wanda kwantiraginsa ta kare a kaka mai zuwa.