Dangote zai kori Wenger idan ya sayi Arsenal

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dangote mai goyon bayan Arsenal ne, wanda ke son sayen hannun jarin kungiyar

Attajirin dan kasuwar nan na Najeriya, Aliko Dangote, ya ce abin da zai fara yi da zarar ya sayi Arsenal shi ne ya kori kociyan kulob din, Arsene Wenger.

Dangote ya ce zai taya kulob din da zarar ya kammala matatar man da yake ginawa a Legas, in ji Bloomberg.

Dangote dai ya dade da kasancewa mai goyon bayan kulob din tun shekarun 1980.

A karshen kakar Premier da ta kare Arsenal ta yi ta biyar a kan teburi, kuma karon farko kenan tun bayan shekara 20, hakan ya sa za ta buga kofin Europa a bana.

Arsenal ta kara tsawaita zaman Arsene Wenger a Emirates zuwa shekara biyu, duk da rabon da kungiyar ta lashe kofin Premier tun kakar 2003/04.

Arsenal ta dauki 'yan wasa biyu a kakar bana da suka hada da Alexandre Lacazette da Sead Kolasinac, kuma kungiyar ta ci Leicester City a wasan makon farko a gasar bana.

Labarai masu alaka