Za a fara gasar La Liga ta bana a ranar Juma'a

La Liga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Juma'a za a fara gasar La Liga ta 2017/18

Bayan da Real Madrid ta lashe kofin Spanish Super Cup na bana, inda ta ci Barcelona 5-1 gida da waje, hakan na nufin za a fara wasannin La Liga a Spaniya a kakar 2017/18.

A jadawalin da aka tsara Valenciya ce za ta karbi bakuncin Las Palmers da fafatawa tsakanin CD Leganes da Deportivo Alavesa a wasan makon farko a ranar Juma'a.

Sai a ranar Asabar Celta de Vigo za ta kece raini da Real Sociedad da karawar da Atletico de Madrid za ta ziyarci Girona da fafatawa tsakanin Sevilla da RCD Espanyol.

Wasannin da za a yi ranar Lahadi kuwa guda uku ne ciki har da wanda Barcelona za ta karbi bakuncin Real Betis da karawar da Real Madrid za ta ziyarci Deportivo La Coruna.

Za a karasa wasannin makon farko a ranar Litinin inda za a kece raini tsakanin Levante da Villarreal da wasa tsakanin Malaga da SD Eibar.

Real ce mai rike da kofin La Liga da aka kammala a kakar 2016/17, kuma na 34 jumulla da ta lashe, Barcelona tana da shi guda 24 sai Atletico mai La Liga guda 10.

Ga jadawalin makon farko a gasar La Liga ta 2017/18:

  • 18/8 CD Leganes da Deportivo Alaves
  • 18/8 Valencia C.F da Las Palmas
  • 19/8 Celta de Vigo da Real Sociedad
  • 19/8 Girona da Atletico de Madrid
  • 19/8 Sevilla FC da RCD Espanyol
  • 20/8 Athletic de Bilbao da Getafe CF
  • 20/8 FC Barcelona da Real Betis
  • 20/8 Deportivo La Coruna da Real Madrid CF
  • 21/8 Levante da Villarreal CF
  • 21/8 Malaga CF da SD Eibar

Labarai masu alaka