Real Madrid ta fi karfin Barcelona – Pique

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pigue wanda ya koma Barcelona daga Manchester United ya yi shekara tara a Barcelona

Mai tsaron bayan Barcelona Gerard Pique ya ce yana jin Real Madrid sama take da su a karon farko, bayan da ta doke su a Spanish Super Cup.

Madrid wadda ke rike da kofin La Liga da na Zakarun Turai na bara ta ci Barca 2-0 a ranar Laraba, kuma tun a ranar Lahadi Madrid din ta doke Barca 3-1 a Nou Camp.

Pique mai shekara 30, wanda ya yi kakar wasa tara a Barcelona ya ce ''Bama kan ganiyar wasa a matsayin kungiya ko kulob''.

''Amma akwai damar da za mu gyara kura-kuren mu, ya kamata mu ci gaba da wasa tare domin samun ci gaban kungiyar''.

Real ta buga karawar ba tare da Cristiano Ronaldo ba, sakamakon dakatar da shi da aka yi daga buga wasa biyar, bayan da aka ba shi jan kati a wasan farko a Nou Camp.

Labarai masu alaka