Gwarzon dan kwallon duniya: Messi da Ronaldo

Fifa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Messi da Ronaldo suna cikin 'yan takarar gwarzon dan kwallon kafa na Turai na bana

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta bayyana sunayen 'yan wasan da za a zabo wanda babu kamarsa a fagen tamaula a shekarar nan.

Cikin 'yan wasan har da Cristiano Ronaldo na Real Madrid wanda ya lashe gasar bara, da Lionel Messi na Barcelona da Neymar wanda Paris St-Germain ta saya mafi tsada a duniya a bana.

Hakazalika, dan kwallon da ya buga wa Manchester United Zlatan Ibrahimovic, a kakar da aka kammala, yana cikin jerin.

Masu horar da tamaula da wasu fitattun 'yan jarida na daga cikin wadanda za su zabo gwarzon dan kwallon kafa na duniya a bana.

A ranar 7 ga watan Satumba za a rufe kada kuri'a, sannan a bayyana wanda ya lashe kyautar a ranar 23 ga watan Octoba a Landan.

Ga jerin 'yan wasan da ke takara:

 • Pierre-Emerick Aubameyang (Borussia Dortmund da Gabon)
 • Leonardo Bonucci (AC Milan da Italy)
 • Gianluigi Buffon (Juventus da Italy)
 • Daniel Carvajal (Real Madrid da Spain)
 • Paulo Dybala (Juventus da Argentina)
 • Antoine Griezmann (Atletico Madrid da France)
 • Eden Hazard (Chelsea da Belgium)
 • Zlatan Ibrahimovic (tsohon dan wasan Manchester United da Sweden)
 • Harry Kane (Tottenham da England)
 • Andres Iniesta (Barcelona da Spain)
 • N'Golo Kante (Chelsea da France)
 • Toni Kroos (Real Madrid da Germany)
 • Robert Lewandowski (Bayern Munich da Poland)
 • Marcelo (Real Madrid da Brazil)
 • Lionel Messi (Barcelona ada Argentina)
 • Luka Modric (Real Madrid da Croatia)
 • Keylor Navas (Real Madrid da Costa Rica)
 • Manuel Neuer (Bayern Munich da Germany)
 • Neymar (Barcelona da Brazil)
 • Sergio Ramos (Real Madrid da Spain)
 • Cristiano Ronaldo (Real Madrid da Portugal)
 • Alexis Sanchez (Arsenal da Chile)
 • Luis Suarez (Barcelona da Uruguay)
 • Arturo Vidal (Bayern Munich da Chile)

Labarai masu alaka