Mece ce makomar Costa da Coutinho?

Diego Costa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Diego Costa na neman komawa Atletico Madrid

Tottenham na daf da sayen dan wasan Ajax mai shekara 21, Davinson Sanchez, in ji Telegraph.

Manchester City ta shirya domin ta bai wa West Brom fam miliyan 22 don sayen keftin dinta dan shekara 29 Jonny Evans, bayan an yi watsi da tayin fam miliyan 18 da ta yi. Kazalika City ta shirya domin ta kusan rubanya albashin dan wasan Arewacin Ireland na fam 75,000 a ko wane mako, in ji Mirror

An yi watsi da tayin da Chelsea ta yi na fam miliyan 63 ga dan wasan Jueventus mai shekara 26 Alex Sandro, in ji Mirror

Daraktan wasannin Barcelona, Robert Fernandez, ya ce zai yi wuya a iya sayen dan wasan tsakiyar Liverpool mai shekara 25, Philippe Coutinho, domin babu damar sallama a yarjejeniyarsa, in ji Liverpool Echo

Barca za ta ci gaba da gwagwarmaya wajen sayen dan wasan Brazil Coutinho, har sai lokacin da aka rufe kasuwar 'yan wasa yayin da ake ci gaba da tsammanin Barcelona za ta sake taya dan wasan, in ji Telegraph

Dan wasan gaban Chelsea, Diego Costa, mai shekara 28, ya ce ba zai sake komawa Stamford Bridge ba, kuma yana son ya sake komawa Atletico Madrid, in ji Telegraph

Everton za ta iya yunkurin daukar aron dan wasan Spaniya Costa daga zakarun Firimiya, in ji Sun.

Dan wasan bayan Spurs Kevin Wimmer, mai shekara 24, yana tattaunawa da West Brom kan yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 15, in ji Telegraph

Ita ma Stoke tana shaukin sayen dan wasan Austria Wimmer, in ji Stoke Sentinel

Dan wasan bayan Arsenal da Brazil Gabriel, mai shekara 26, yana dab da komawa Valencia a wata yarjejeniyar kudi fam miliyan 10, in ji Evenin Standard

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fabinho ya koma Monaco da taka leda ne ranar 19 ga watan Yunin shekarar 2013

Paris St-Germain na shaukin sayen dan wasan Monaco mai shekara 23, Fabinho, in ji L'Equipe

Dan wasan tsakiyar PSG Blaise Matuidi, mai shekara 30, ya kammalawa gwaje-gwaje a Juventus, amma kawo yanzu kungiyoyin biyu ba su amince a kan yadda za a biya kudin cinikinsa ba. Jagoran PSG Unai Emery, bai so ya sayar da dan wasen ba, in ji Le Parisien

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An dade ana kiki-kaka kan makomar Ousmane Dembele

Shugaban Borussia Dortmund ya ce Barcelona ba ta zo kusa da kudin da kungiyar ta saka wa dan wasan gaban Faransa mai shekara 20 Ousmane Dembele, in ji Kicker

Fiorentina ta shaida wa dan wasan Croatia mai shekara 29 Nikola Kalinic, wanda AC Milan take hako, cewar ba za a ci taranshi ba bayan ya kasa zuwa atisaye ranar Alhamis, in ji Sun

Sunderland na fuskantar barzanar rasa Didier Ndong, mai shekara 23, domin Lyon ka iya taya dan wasan tsakiyar idan ta kasa sayan dan wasan Celta Vigo, Pape Cheikh Diop, in ji Daily Star

Southampton ta yi kusa da sayan dan wasan bayan Lazio, Wesley Hoedt, mai shekara 23, bayan ta taya shi kan kudi fam miliyan 15, in ji Daily Mail

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Me ya sa Man Utd ta hakikance akan sayan Perisic ne?

Manchester United ba ta yanke kauna ba kan sayen dan wasan gefe Ivan Perisic, mai shekara 28, duk da cewar fam miliyan 39 ne tayin da suka yi wa Inter Milan, in ji Mirror

Labarai masu alaka