Tottenham na dab da sayen Davinson Sanchez

Image caption Sanchez ne zai zama na farko da kulob din zai saya a lokacin bazara.

Tottenham na dab da daukar Davinson Sanchez daga kulob din Ajax, a kan kudin da ake sa ran zai kai fam miliyan 42.

Sanchez mai shekara 21 shi ne zai zama na farko da kulob din zai saya a lokacin bazara.

Kociyan Tottenham Mauricio Pochettino ya ce, yana son sayen 'yan kwallo hudu kafin a rufe kasuwar tamaular, kuma yana sa ran zai kara wasu 'yan wasan".

Labarai masu alaka