Jese Rodriguez ya ci Arsenal

Stoke Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Stoke City ta ci kwallo dayan da ya ba ta damar samun maki uku a karawar

Tsohon dan wasan Real Madrid, Jese Rodriguez ne ya ci Arsenal a wasan farko da ya buga wa Stoke City a mako na biyu a gasar Premier a ranar Asabar.

Jese ya koma Stoke ne da murza-leda karkashin koci Mark Hughes daga Paris St-Germain a ranar Laraba.

Dan wasan ya kuma ci Arsenal ne a bugun kwallon da Saido Berahino ya yi masa, bayan da aka koma wasa na biyu bayan hutu da 'yan kwallon suka yi.

Wannan ne karon farko da Stoke ta ci wasa a bana, ita kuwa Arsenal ta ci Leicester City a makon jiya.