Ebola ya buge Dogon Bunza
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ebola ya buge Dogon Bunza

Abdurrazak Ebola ya buge Dogo na dan Bunza a turmin farko a damben safiyar Lahadi da suka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Turmi daya suka taka Ebola daga Kudu ya yi nasara, inda daga baya Dan Bunza daga Arewa ya ce zarensa ya kwance kafin a buge shi, amma daga baya ya amince an kashe shi.

Mohammed Abdu ne ya hada rahotan:

Ga sakamakon wasu wasannin da aka yi babu kisa:

  • Sani Mai kifi daga Arewa da Dogon Aleka daga Kudu
  • Shagon Langa-Langa daga Arewa da Shagon Mai Keffi daga Kudu
  • Shagon Caka-Caka daga Arewa da Shagon Sama'ila daga Kudu
  • Sanin Kwarkwada daga Kudu da Aminun Mahaukacin Teacher