Real Madrid za ta ziyarci Deportivo

La Liga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasan farko da Real za ta buga a gasar La Liga ta 2017/18

Deportivo La Coruna za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan makon farko a gasar La Liga ta Spaniya ta 2017/18 a ranar Lahadi.

A bara a kakar 2016/17, Deportivo ce ta fara ziyartar Madrid, inda ta yi rashin nasara da ci 3-2 a Santiago Bernabeu a ranar 10 ga watan Disambar 2016.

A wasa na biyu da suka kara Real ce ta casa Deportivo har gida da ci 6-2, sai dai Ronaldo ba zai buga wasan na ranar Lahadi ba, sakamakon dakatar da shi buga wasa biyar da aka yi.

Cristiano Ronaldo zai yi hutun dole

Real Madrid ce ta lashe kofin La Liga na bara da aka kammala, kuma kungiyar ta ci UEFA Super Cup da Spanish Super Cup a bana.

Wasannin da za a yi a ranar Lahadi:

Athletic de Bilbao da Getafe

FC Barcelona da Real Betis

Deportivo La Coruna da Real Madrid CF

Labarai masu alaka