Ina so na dade a Chelsea — Conte

Chelsea Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Conte ya lashe kofin Premier a kakar farko da ya ja ragamar Chelsea

Antonio Conte ya ce yana fatan zai dade yana horar da Chelsea shekara da yawa, kuma zai yi murna idan aka fadada filin Stamford Bridge yana tare da kungiyar.

Conte ya koma jan ragamar Chelsea a bara kan yarjejeniyar shekara uku, yana kuma fatan ya kara tsawaita zamansa a Stamford Bridge din a nan gaba.

Chelsea na shirin neman izinin fadada filin wasanta da wajen zaman 'yan kallo, amma har yanzu bata yanke shawarar ko ta ci gaba da shirin ko akasin hakan.

Koci da ya dade yana horar da Chelsea shi ne John Neal wanda ya yi aiki tsakanin 1981 zuwa 1985.

Conte ya ce ''Ina son na kafa tarihin dade wa a kungiyar, kuma abin da zan fuskanta kenan''

Kocin ya ja ragamar kungiyar a kakar farko inda ta ci kofin Premier.

Labarai masu alaka