Barcelona ta samu maki a kan Betis

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta ci Betis ta kuma hada maki uku da kwallaye biyu a raga
Barcelona ta doke Real Betis a wasan makon farko a gasar La Liga ta kakar 2017/18 da suka fafata a Nou Camp a ranar Lahadi.
Alin Tosca ne ya ci a minti na 36 da fara tamaula, sannan Barcelona ta kara ta biyu saura minti shida a tafi hutun rabin lokaci.
Da wannan nasarar, Barcelona za ta ziyarci Deportivo Alaves a wasan mako na biyu a ranar 26 ga watan Agusta.
Barcelona wadda ta ci International Champions Cup a Amurka a bana ta sha kashi a hannun Real Madrid 5-1 gida da waje a gasar Spanish Super Cup.