Real Madrid ta caskara Deportivo

La Liga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gareth Bale ne ya fara ci wa Real Madrid kwallo a Deportivo

Deportivo La Coruna ba ta ji da dadi ba a gidanta a hannun Real Madrid, inda aka doke ta da ci 3-0 a wasan makon farko a gasar La Liga ta kakar bana ta 2017/18.

Real ta fara cin kwallo ta hannun Gareth Bale minti 20 da fara tamaula kuma minti bakwai tsakani ta ci ta biyu ta hannun Casemiro.

Bayan da aka dawo daga hutu ne da minti 17, Madrid ta kara kwallo na uku a raga ta hannun Toni Kroos.

Sai dai Madrid ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili bayan da aka bai wa Sergio Ramos jan kati daf da za a tashi.

Sai dai Ronaldo bai buga wasan ba, sakamakon dakatar da shi da aka yi daga buga wasa biyar.

Madrid wadda ke rike da kofin gasar da aka kammala za ta buga wasan mako na biyu a Santiago Barnebeau da Valencia a ranar 27 ga watan Agusta.

Madrid ta ci kofin UEFA Super Cup bayan da ta doke Manchester United ta kuma dauki Spanish Super Cup bayan da ta yi nasarar cin Barcelona gida da waje a bana.

Labarai masu alaka