Wold Cup Under 17: Rwanda za ta karbi bakunci

Rwanda
Image caption Nzamwita ya ce Rwanda za ta iya karbar bakuncin babbar gasar kwallon kafa

Hukumar kwallon kafa ta Rwanda (Ferwafa) na shirin kammala shiga jerin masu son karbar bakuncin gasar kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekara 17 da za a yi a shekarar 2019.

Shugaban hukumar, Vincent Nzamwita ya jaddada cewar kasar za ta iya karbar bakuncin babbar gasar kwallon kafa.

Nzamwita ya shaida wa BBC cewa, "Tuni muka gabatar da bukatarmu a hukumance ga FIFA, kuma sun yi mana rajista tare da ba mu takardun amincewa da tayin namu."

Nzamwita ya ce, karbar bakuncin gasar cin kofin duniya za ta daga darajar kasar, har da yankin nahiyar baki daya.

A bara ma kasar ta karbi bakuncin gasar cin kofin zakarun Afirka wato (CHAN), ta 'yan wasan da ke murza-leda a Afirka, inda sama da mutum 200,000 daga sassan nahiyar Afirka suka halacci wasannin.

A ranar 6 ga watan Oktoban 2017 ne za a fara gasar cin kofin matasa 'yan kasa da shekara 17, wacce ta hada kasashe 24, inda Ghana da Guinea da Mali da Niger za su wakilci Afirka.

Labarai masu alaka