Lucas Vazquez ya yi wa Madrid wasa 50

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ta ci UEFA da Spanish Super Cup a bana

Bayan da Real Madrid ta ci Deportivo La Corunya 3-0 a wasan makon farko a gasar cin kofin La Liga a ranar Lahadi, dan wasanta Lucas Vazquez ya buga mata wasa na 50 a ranar.

Dan kwallon ya fara buga wa Madrid tamaula a ranar 12 ga watan Satumba 2015 a karawar da ta doke Espanyol 6-0, inda ya shiga wasan daga baya.

Mako daya tsakani aka fara wasa da shi a fafatawar da Granada ta doke Madrid 1-0, sannan ya fara ci wa Madrid kwallo a karawar da ta doke Real Sociedad 3-1 a ranar 30 ga watan Satumbar 2015.

Dan wasan ya ci kofin zakarun Turai biyu a Madrid da kofin duniya na zakarun nahiyoyi da UEFA Super Cup biyu da La Liga da na Spanish Super Cup.

Labarai masu alaka