Real Madrid za ta kara da Fiorentina

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Sau 26 Real Madrid ta ci Santiago Bernabeu Trophy

Kungiyar Real Madrid za ta fafata da Fiorentina a gasar Santiago Bernabeu Trophy a ranar Laraba.

Madrid ta ci kofin sau 11 a jere, kuma rabon da a doke ta a wasannin tun 2004, sannan ta lashe shi sau 26 jumulla.

Wannan karawar da Madrid za ta yi da Fiorentina ita ce ta 38 a gasar, kuma cikin 'yan wasan da suke buga mata tamaula su biyar a yanzu sun ci mata kwallaye a fafatawar.

'Yan wasan sun hada da Benzema wanda ya ci biyar da Ramos da Nacho kowannnensu ya ci biyu-biyu sai Marcelo da kuma Isco da suka ci dai-dai.

Tun bayan da Madrid ta yi rashin nasara a hannun Pumas a gasar, ta ci hadakar 'yan wasan da ke buga gasar Amurka da Anderlecht da Partizan da Sporting Clube na Portugal da Rosenborg da Penarol da Millonarios da Al-Sadd da Galatasaray sau biyu da kuma Stade de Reims.

Ga jerin 'kungiyoyin da suka lashe kofin:

  • Real Madrid 26
  • Bayern Munich 3
  • Milan 2
  • Inter 2
  • Hamburg 1
  • Dynamo Kiev 1
  • Ajax 1
  • Pumas 1