Barcelona na yi wa Neymar 'bi-ta-da-kulli'

PSG Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Neymar ya ci kwallo uku tun komawarsa PSG

Barcelona ta yi karar tsohon dan wasanta Neymar kan kudin ladan wasa fam miliyan 7.8.

Neymar ya koma Paris St Germain kan kudi fam miliyan 200 a matsayin wanda aka saya mafi tsada a bana.

Dan kwallon tawagar Brazil ya koma Faransa da murza-leda bayan da ya biya kunshin yarjejeniyarsa a Barcelona wacce ta gindaya idan za a saye shi.

''Barcelona ta bukaci ya dawo da ladan wasan da tuni aka biya shi tun da bai kammala yarjejeniyarsa a Spaniya ba''.

Bayan fam miliyan 7.8 da kungiyar ta bukaci dan wasan ya biya, ta kuma nemi ya biya tarar kaso 10 cikin dari na lattin mayar mata da kudin da bai yi ba.

Barcelona ta kuma bukaci Paris St-Germain ta dauki alhakin biyan kudin idan Neymar ba zai yi da kansa ba.

A ranar 11 ga watan Agusta Barcelona ta shigar da karar a kotu ta musamman da ta danganci harkar kwadago.

Labarai masu alaka