Ni nake bin Barcelona kudi — Neymar

Neymar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Neymar ya ci kwallo uku a PSG a wasa biyu da ya buga mata a gasar Faransa

Dan kwallon Paris St-Germain, Neymar zai kalubalanci Barcelona kan kararsa da ta shigar a Spaniya.

Barcelona na son dan kwallon ya biya fam miliyan 7.8 ladan wasa da aka ba shi a lokacin da ya tsawaita yarjejeniyar zama a kungiyar zuwa shekara biyar, wata tara kafin ya koma Faransa.

Dan wasan na Brazil ya koma PSG a cikin watan Agusta kan fam miliyan 200, bayan da ya biya kunshin yarjejeniyar da Barcelona ta ce sai an biya idan kwantiraginsa bai kare ba.

Lauyan Neymar zai kalubalanci Barcelona kuma ya fitar da zawabin dan kwallon mai shekara 25.

Neymar ya ce shi ne yake bin Barcelona kudi bisa barin Nou Camp, ba wai ita ce ke neman hakki a wajensa ba.

A jawabin da suka fitar ''Kan ladan wasan da Neymar ke bin Barcelona a yarjejeniyar 2016, yana da muhimmaci na sanar da cewar dan wasan ya fara shirin yadda zai karbi hakkinsa a kotunan da suka da ce''.

A ranar Talata Barcelona ta bukaci Neymar ya dawo da ladan wasa da ''tuni ta biya shi'' da karin kaso 10 cikin dari kan lattin kin biyan kudin.

''Kungiyar tana neman ya biyata kudin ne, saboda bai karasa yarjejeniyar da ya kulla da ita ba'' kamar yadda ta ce.

Labarai masu alaka