Super Eagles ta gayyaci Mikel Obi da 'yan wasa 22

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Obi bai buga wasan da Afirka ta Kudu ta ci Nigeria a gida ba

Kocin tawagar kwallon kafa na Nigeria, Gernot Rohr ya gayyaci kyaftin Mikel John Obi da Odion Ighalo cikin jerin 'yan wasan da za su buga wa kasar karawa da Kamaru.

Nigeria za ta karbi bakuncin Kamaru a ranar 1 ga watan Satumba a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo a wasan shiga gasar kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci a 2018.

Super Eagles ce ta daya a rukuni na biyu da maki shida bayan da ta yi nasara a kan Zambia da Algeria, Kamaru ce ta biyu da maki biyu wacce ta yi kunnen doki da Algeria ta tashi babu ci da Zambia.

'Yan wasan da aka gayyata tawagar Nigeria:

Masu tsaron raga: Daniel Akpeyi (Chippa United, South Africa); Ikechukwu Ezenwa (FC IfeanyiUbah); Dele Alampasu (Cesarense FC, Portugal)

Masu tsaron baya: William Ekong (Bursaspor FC, Turkey); Abdullahi Shehu (Anorthosis Famagusta, Cyprus); Leon Balogun (FSV Mainz 05, Germany); Tyronne Ebuehi (ADO Den Haag, The Netherlands); Elderson Echiejile (Sivasspor FC, Turkey); Chidozie Awaziem (Nantes FC, France); Ola Aina (Hull City, England)

Masu wasan tsakiya: Mikel John Obi (Tianjin Teda, China); Ogenyi Onazi (Trabzonspor FC, Turkey); Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Oghenekaro Etebo (CD Feirense, Portugal); John Ogu (Hapoel Be'er Sheva, Israel); Mikel Agu (Bursaspor FC, Turkey)

Masu cin kwallo: Ahmed Musa (Leicester City, England); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Moses Simon (KAA Gent, Belgium); Alex Iwobi (Arsenal FC, England); Odion Ighalo (Chang Chun-Yatai, China); Victor Moses (Chelsea FC, England); Anthony Nwakaeme (Hapoel Be'er Sheva, Israel)

Masu jiran kar-ta-kwana: Uche Agbo (Standard Liege, Belgium); Henry Onyekuru (Anderlecht FC, Belgium); Kenneth Omeruo (Chelsea FC, England); Aaron Samuel (CSKA Moscow, Russia); Alhassan Ibrahim (Akwa United); Stephen Eze (FC IfeanyiUbah); Ifeanyi Ifeanyi (Akwa United)