Rooney ya bar buga wa Ingila Tamaula

England Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rooney ya fara buga wa Ingila tamaula a Fabrairun 2003

Dan wasan da ke kan gaba wajen ci wa tawagar kwallon kafa ta Ingila kwallaye a tarihi, Wayne Rooney ya yi ritaya daga buga mata wasannin.

Kocin Ingila, Gareth Southgate ya gayyaci Rooney domin ya buga karawar da kasar za ta yi da Malta da kuma Slovakia.

Sai dai Rooney mai wasa a Everton mai shekara 31 ya ce ''Ina alfahari a duk lokacin da aka mika min goron gayyata, amma yanzu lokaci ya yi da ya kamata na yi ritaya''.

Tsohon kyaftin din Manchester United ya ci wa Ingila kwallo 53 a wasa 119 da ya yi mata.

Rooney ya fara buga wa Ingila wasa a fafatawar da ta yi da Australia a Upton Park a watan Fabrairun 2003 inda ta ci karawar da ci 3-1.

Dan wasan ya sanar da yin ritayar ne kwana biyu da ya ci kwallo na 200 a gasar Premier a wasan da Everton ta tashi 1-1 da Manchester City a Ettihad.

Labarai masu alaka