Champions League: Za a raba jadawali ranar Alhamis

Champions League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rea;l Madrid tana da kofin Zakarun Turai guda 12

A ranar Alhamis za a raba jadawalin wasannin cin Kofin Zakarun Turai kakar 2017/18 da za a gudanar a Monaco.

Idan aka zo yin bikin, babu kungiyar da za ta kara da wadda take kasa daya a wasannin rukuni, yayin da mahukunta za su sanar da yadda za a raba kungiyoyin.

Da zarar an raba jadawalin ake sa ran fara wasannin cikin rukuni tsakanin 12 zuwa 13 ga watan Satumba, za kuma a yi wasan karshe a watan Mayu a Kyiv.

Haka kuma a lokacin ne za a bayyana dan wasan da ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa da babu kamarsa a Turai a shekarar nan da sauran kyaututtuka.

Real Madrid ce ke rike da kofin Zakarun Turai na 2016/17 na 12 da ta dauka jumulla.

Labarai masu alaka